Sashen shari'a na Gidauniyar Wikimedia/sabuntawar ToU 2023/Sabuntawar da aka gabatar
An amince da wannan sabuntawar wadda aka gabatar kuma an haɗa shi azaman Sharuɗɗan Amfani da Wikimedia, mai tasiri ga Yuni 7, 2023 ( sanarwar amincewa karanta). |
Taƙaitawa
Ɓangaren ƙudurin mu shine:
- Ƙrfafawa tare da cicciɓa mutane a faɗin duniya domin tattara da haɓaka abun ciki na ilimi kuma ko dai buga shi ƙarƙashin lasisin kyauta ko sadaukar da shi ga jama'a.
- Watsawa wannan ƙunshiyar yadda ya kamata kuma a duniya, kyauta.
- Bayarwa gidajen yanar gizo da kayan aikin fasaha don taimaka muku yin wannan.
Kana da damar
- Karantawa da buga maƙalolin mu da sauran bayanan mu a kyauta.
- Rabawa da sake amfani da maƙalolin mu da sauran kayan mu ƙarƙashin lasisi buɗaɗɗe kuma na kyauta.
- Bayar da gudunmawar gyara shafukan mu ko aiyukan mu.
A ƙarƙashin waɗannan sharuɗɗa:
- Alhaki - Kuna ɗaukar alhakin gyare-gyarenku (tunda mu kawai karɓar baƙuncin abubuwan ku ne kawai).
- Civility - Kuna goyan bayan mahallin farar hula kuma kada ku cutar da sauran masu amfani.
- Halayen Halal - Ba ku keta haƙƙin mallaka, buga abubuwan da ba bisa ka'ida ba, ko keta wasu dokokin da suka dace waɗanda ke bin ƙa'idodin haƙƙin ɗan adam.
- Babu cutarwa - Ba ku cutar da kayan aikinmu na fasaha ba kuma kuna bin manufofin wannan kayan aikin.
- Sharuɗɗan Amfani da Manufofin - Kuna bin waɗannan Sharuɗɗan Amfani na ƙasa, zuwa ƙa'idodin ɗabi'a na duniya, da manufofin al'umma masu dacewa lokacin da kuka ziyarci gidajen yanar gizon mu ko Ayyuka ko shiga cikin al'ummominmu.
Tare da fahimtar hakan:
- Za ku bayar da kyautar Lasisin Gudunmawar ku - Gabaɗaya dole ne ku ba da lasisin gudummawar ku da gyare-gyare ga gidajen yanar gizon mu ko Ayyuka a ƙarƙashin lasisin buɗaɗɗe kuma kyauta (sai dai idan gudummawar ku tana cikin jama'a).
- Babu Shawarar Ƙwararru - Abubuwan da ke cikin labaran kan Wikipedia da sauran Ayyuka don dalilai ne na bayanai kawai kuma baya zama shawarar ƙwararru.
Idan kana buƙatar temako ko kuma kana so kayi ƙorafi game da waɗannan sharuɗɗan amfanin kana iya:
- Neman temako a kan aiyukan mu: Danna "temako" a gefen hagu na mafi yawancin shafukan.
- Neman temako ta imel: Tuntuɓi ƙwararren mai amfani ta imel info@wikimedia.org.
- Tuntuɓi Gidauniyar Wikimedia: Zaka iya bincikar mu a shanfin tuntuɓar mu.
- Idan kai sabon mai bayar da gudummawa ne: Zaka iya neman ƙa'idodin aiyukan domin su taimaka maka koyon yadda zaka yi amfani da aiyukan Wikimedia a shafuka kamar na farko don masu shigowa.
Sharuɗɗan Amfani
'Ka yi tunanin duniyar da kowane ɗan adam zai iya raba wani adadi na ilimi. Wannan shine sadaukarwarmu.'- Bayanin Hangen Mu
Barka da zuwa Wikimedia! Wikimedia Foundation, Inc. ("mu" ko "mu"), ƙungiya ce mai zaman kanta, mai hedikwata a San Francisco, California, Amurka, manufar waye ta ba da ƙarfi da sa mutane a duk duniya don tattarawa da haɓaka abun ciki a ƙarƙashin lasisi kyauta ko a cikin jama'a, da kuma yada shi yadda ya kamata kuma a duniya, kyauta.
Domin tallafawa al'ummarmu masu fa'ida, muna samar da mahimman abubuwan more rayuwa da tsarin tsari don haɓaka ayyukan wiki na harsuna da yawa da bugu nasu (kamar yadda aka bayyana akan Wikimedia) <(ta haka ake kira "Ayyuka") da sauran yunƙurin da ke hidimar wannan manufa. Muna ƙoƙari don yin da kiyaye abubuwan ilimi da bayanai daga Ayyukan da ake samu akan yanar gizo kyauta, a cikin har abada.
Muna muku maraba (“kai” ko kume “mai amfani da shafi”) a matsayin mai karatu, ko kuma muna karfafa muki gwiwa da ku shiga cikin al’ummar Wikipedia. Kafin ku fafata a cikin gasar, ko yaya, muna jawo hankalinku da ku karanta kuma ku aminci da wadannan Ka’idojin Amfani (“Ka’idojin Amfani da shafi”).
Bayani
Waɗannan Ka’idoji na Amfani suna bayani ne akan harkokinmu na jama’a a Gidauniyar Wikipedia, that kuma hakkoki da nauyi da ke tafiyar damu duka. Muna daukan nauyin abubuwa da dama na ilimi da bayanai, wadanda duka mutane ne kamar ku ke bada gudummawa kuma suke tabbatar da wanzuwarsu. A gabaki daya, mu bamu bada gudummawa, ko kuma lura da, ko kuma goge bayanai (sai dai a wasu lokuta kadan, kamar a karkashin dokoki kamar wannan Ka’idoji na Amfani da shafi, don hadin kai na shari’a, ko kuma a lokacin da aka fuskanci barazana na gaggawa wanda ka iya kawo lahani mai tsanani). Wannan na nuna cewa kula da sauye-sauye sun rataya ne akan ku da sauran ‘yan uwanku masu bada gudummawa wanda ke kirkira kuma suke kula da bayanai.
Al’ummar Wikipedia - cibiyar sadarwa ce na masu bada gudummawa wadanda suke tsaye wajen bunkasaqa da kuma amfani da shafukan Wikipedia da/ko kuma shafukansu na yanar gizo (wadanda ake kira “Project Websites”) - muhimman hanyoyi ne ta yadda ake cimma kudurorin shafin. Wannan al’ummar kuwa suna bayar da gudummawa da kuma taimakawa wajen gudanar da Shafuka da kuma Shafukan Yanar-gizo. Wannan al’ummomi har wayau suke gudanar da muhimman ayyuka na kirkira da kuma tilasta dokoki ga kowacce shafi daga cikin shafukanmu. (Kamar irinsu shafukan yaruka daban daban na shafukan Wikipedia ko kuma shafukan Wikimedia Commons na yaruka da dama).
Muna maraba da kai/ke, masu amfani da shafi, wajen shiga a matsayin mai bayar da gudummawa, edita, ko kuma mai wallafawa, amma zaku bi dokoki da ke gudanar da kowacce shafi mai zaman kanta, wanda suka hada da Universal Code of Conduct (UCoC), wacce ta shafa daukakin shafukan Wikimedia. Shafin mafi girma itace Wikipedia, duk da haka muna daukan nauyin wasu shafukan da dama, kowanne da nasu kudurorin da kuma salon sarrafasu. Kowanne nau’i na shafi na dauke da nasu gungun masu bayar da gudummawa, editoci, da kuma masu wallafawa wanda ke aiki tare don kirkira da kuma kula da bayanai a wannan Shafin. Muna maraba da ku don shiga wadannan kungiyoyi kuma kuyi aiki da su don inganta wadannan Shafuka. Tunda mun sadaukar wajen isar da bayanai kyauta ga al’umma, ana mayar da bayanai da kuke shigarwa ta hanyr gudummawarku kyauta a karkashin lasisin ko kuma ana sakinau a karkashin public domain.
Ku da cewa ku ke da alhakin kowanne gudummawa, gyararraki da kuma sake amfani da bayanan Wikimedia da kuka bada a shariance a karkashin dokokin Kasar Amurka da kuma sauran dokoki da suka jibancesu (wanda suka hada da dokoki inda ku ko kuma wadanda kuka rubuta bayanai akansu). Hakan na nufin cewa yana da muhimmanci ku kiyaye sosai dangane da abubuwan da kuke sanyawa, sauyawa ko kuma sake amfani da bayanai. Dangane da wadannan nauyi, muna da wasu dokoki akan abubuwan da bazaku iya yi ba, wanda yawancinsu sun kasance ko dai don kariyarku ko kuma don kariyar wasu masu amfani da shafin kamar ku. Kuma ku sanya a ranku cewa wadannan bayanai da muke daukan nauyi sun kasance don wanzuwar bayanai kadai, saboda haka idan kuna bukatan shawara daga kwararru don wata tambaya (irin na lafiya, doka, ko kuma harkokin kudi), ku nemo taimako daga kwararru wanda suka dace. Har wayau mun hada da sauran muhimman bayanai da kuma ka’idoji, saboda haka ku taimaka ku karanta wadannan Dokokin Amfani gabaki daya.
Don neman karin haske, sauran kungiyoyi irinsu local Wikimedia chapters|Kananan Rukunnai na Wikipedia da sauran kungiyoyi, da ka iya samun kudurori iri daya duk da haka sun kasance masu zaman kansu ne a shari’ance sannan kuma bambanta da Gidauniyar Wikimedia. Face idan ita kanta Gidauniyar ta sanar cewa bangare ne da aka baiwa dama don wani Shafin Ayyukanta, wadannan sauran kungiyoyi basu da alhaki wajen gudanar da harkokin shafukan Yanar-gizo ta Wikimedia ko kum bayanansu.
1. Hidimomin mu
Gidauniyar Wikimedia ta dogara ne wajen karfafa girma, bunkasa, da kuma yadiwar bayanai na ilimi a harsuna daban daban kyauta, da kuma daukan nauyin Ayyukan cikakkun bayanai Ayyukan wadannan shafukan na wiki ga al’umma a kyauta ba tare da sun biya ba. Matsayinmu shine daukan nauyin wasu daga cikin nazarin bayanai mafi girma na hadin gwiwa a duniya, wadanda ake iya samu a nan. Amma duk da haka, muna taka rawa ne kadai a matsayin masu samarda sabis, muna kula da wadatar kayan aiki da kuma tsarin kungiyar. Wadannan kayayyaki na aiki da kuma tsare-tsare ke baiwa masu amfani da shafukanmu wajen gina Shafuka ta hanyar bayar da gudummawa da kuma yin gyare-gyare da kansu. Har wayau, suna ba wa masu amfani da shafukan wajen sake amfani da wadannan bayanai. Kayayyakin aiki da muke kika da su sun hada da kayan fasaha na musamman wadanda ke baiwa masu amfani da shafukan danar cudanya da kuma sake amfani da bayanai a kimiyyance (wanda ake kira “Application Programming Interface” ko kuma “APIs”), da kuma application na wayar hannu
Kamar yadda akayi amfani dasu a daukakin sauran Ka’idojin Amfani, sabis dinmu sun hada da: The Shafun Project da muke daukan nauyi, kayayyakin aiki na fasaha da muke kula da su, da kuma kowanne irin fage na fasaha da muke daukan nauyi don kulawa da kuma bunkasa Shafukanmu.
A dalilin matsayinmu na musamman, akwai wasu ‘yan abubuwa da ya kamata ka sani yayin lura da dangantakar ka da mu, da kuma Shafuka, da kuma sauran masu amfani da shafukan:
- Bamu daukan matsayin masu gyara: Saboda ana gyara Shafukan ne a cikin hadin gwiwa, masu amfani da shafukan ne ke samar da mafi akasarin bayanan da muke daukan nauyi, kuma sannan mu bamu yin gyara ko kadan. Hakan na nufin cewa mu gabaki daya bamu kula da gyararraki, kuma bamu da alhakin kowanne daga cikin wadannan bayanai. Haka zalika, face idan munyi bayani daban, bamu yarda da wani ra’ayi da aka yada ba ta shafukanmu, sannan kuma bamu wakiltar ko kuma tabbatar da gaskiyar, daidai, ko kuma ingancin wani bayani da wata kungiya ta shigar a shafukanmu ba. Ku ke da alhakin duk wani abu da kuka yi: Ku ke da alhakin duk wani gyara da kukayi a shari’ance, sake amfani da wani bayani a shafukanmu, amfani da kuka yi sa APIs, da kuma amfani da sabis dinmu baki daya da dai sauransu. Domin kariyar kanku ku kula sosai don tabbatar da cewa kun kauce wa duk wani aiki da zai janyo tuhuma ko kuma tauye wani hauki a karkashin wadannan dokoki. Domin neman karin haske, dokokin da suka jibance su sun hada da akalla dokokin kasar Amurka da kuma Jihar California. Dangane da sauran wasu kasashe, ana tantance wannan ne a dangane da sabani. Duk da cewa muna iya kin yarda da irin wadannan ayyukan, muna yi wa masu amfani da shafukanmu musamman editoci, masu bayar da gudummawa, da kuma marubuta wadanda ba 'yan kasar Amurka ba doka na iya wanzar da hukuncin kasa a gare ku, wanda suka hada da dokar kasar da kuke rayuwa ko kuma inda kuke duba bayanai ko kuma gyara su. Mu gabaki daya ba zamu iya bayar da kariya ba, tabbaci, tsiratarwa ko kuma biyan kudi dangane da wanzar da wadannan dokoki ba.
2. Sharuɗɗa da ƙa'idodi
Mun buƙata da ka duba Sharuɗɗa da ƙa'idodin mu, saboda haka za ka gane yadda muke karba tare da yin amfani da bayanan ka.
3. Abinda mika Shirya
- Saboda muna karɓar baƙuncin ɗimbin ƙunshiya waɗanda abokan aikinmu suka ƙirƙira ko kuma suka tattara, za ku iya haɗu da abubuwan da kuka ga abin banƙyama, kuskure, yaudara, ɓarna, ko akasin haka. Don haka muna rokon ku yi amfani da hankali da kuma yanke hukunci lokacin amfani da ayyukanmu.
- Abubuwan da ke cikin Ayyukan' domin dalilai na bayanai ne na gaba ɗaya kawai: Ko da yake Ayyukanmu suna ɗaukar nauyin bayanai da yawa waɗanda suka shafi batutuwan ƙwararru, gami da likitanci, shari'a, ko al'amurran kuɗi, an gabatar da wannan ƙunshiyar don dalilai na yau da kullun kawai. Bai kamata a ɗauke shi azaman shawara na ƙwararru ba. Da fatan za a nemi shawarwarin ƙwararrun ƙwararrun masu zaman kansu daga wani wanda ke da lasisi ko kuma ya cancanta a yankin da ake buƙata a madadin yin aiki da kowane bayani, ra'ayi, ko shawara da ke ƙunshe a cikin ɗayan Gidan Yanar Gizon.
4. Kamewa daga Wasu Ayyuka
Ayyukan da Gidauniyar Wikimedia ke shiryawa suna wanzuwa ne kawai saboda ƙwaƙƙwaran al'umma na masu amfani kamar ku waɗanda suka haɗa kai don rubutawa, gyara, da daidaita abubuwan. Muna maraba da shigowar ku cikin wannan al'umma. Muna ƙarfafa ku da ku kasance masu zaman kansu da ladabi a cikin hulɗar ku da wasu a cikin al'umma, kuyi aiki da gaskiya, da kuma yin gyara da gudunmawar da nufin ci gaba da manufar aikin da aka raba. Muna rokon duk masu amfani su duba su bi Ka'idojin Halaye na Duniya ("UCoC"), wanda ke tsara abubuwan buƙatu don kwalejoji, haɗin gwiwar jama'a a duk ayyukan da muke ɗauka.
Wasu ayyuka, na doka ko na doka a ƙarƙashin ƙa'idar da ta dace, na iya zama cutarwa ga sauran masu amfani da keta dokokin mu, kuma wasu ayyukan na iya sa ku ga abin alhaki. Don haka, don kariyar ku da ta sauran masu amfani, ƙila ba za ku iya yin irin waɗannan ayyukan akan, ko amfani da su, Ayyukanmu ba. Waɗannan ayyukan sun haɗa da:
- Cin Mutunci da Cin Zarafin Wasu
- Shiga cikin barazana, zage-zage, batsa, lalata, ko cin zarafi kamar yadda aka bayyana a cikin UCoC;
- Isar da saƙon sarkar, saƙon takarce, ko wasiƙun banza ga wasu masu amfani;
- Buga ko gyara abun ciki tare da niyyar cutar da wasu sosai, kamar jawowa kansa cutarwa da gangan, ko haifar da farfaɗiya da gangan.
- Tauye Sirrin Wasu
- Keta haƙƙin keɓantawa na wasu a ƙarƙashin dokokin Amurka ta Amurka ko wasu dokokin da suka dace (waɗanda ƙila sun haɗa da dokokin inda kuke zama ko inda kuke kallo ko shirya abun ciki);
- Neman bayanan da za'a iya tantancewa don dalilai na tsangwama, cin zarafi, ko keta sirrin sirri, ko don duk wata talla ko kasuwanci da Gidauniyar Wikimedia ba ta amince da ita ba; kuma
- Neman bayanan da za a iya tantancewa daga duk wanda bai kai shekara 18 ba, ko kuma wanda bai kai shekaru 18 ba, don haramtacciyar manufa ko keta duk wata doka da ta shafi lafiya ko jin daɗin yara kanana.
- Shiga Cikin Kalaman Ƙarya, Kwaikwaya, ko Zamba
- Buga abun ciki da gangan ko da gangan wanda ya ƙunshi batanci ko batanci a ƙarƙashin dokokin Amurka;
- Buga ko gyara abun ciki da niyyar yaudara ko yaudarar wasu;
- Ƙoƙarin yin koyi da wani mai amfani ko mutum ɗaya, bata sunan alaƙar ku da kowane mutum ko mahaluki, ɓoye alaƙar ku da kowane mutum ko mahaluƙi lokacin da ake buƙatar bayyanawa ta waɗannan sharuɗɗan ko manufofin aikin gida, ko amfani da sunan ko sunan mai amfani na wani tare da niyyar yaudara; kuma
- Aikata zamba.
- Aikata Cin Haƙƙin Ƙirar Hankali
- Cin zarafin haƙƙin mallaka, alamun kasuwanci, haƙƙin mallaka, ko wasu haƙƙoƙin mallaka a ƙarƙashin doka mai aiki.
- Rashin yin amfani da Sabis ɗinmu don Wasu Manufofin Ba bisa ka'ida ba
- Wallafa hotunan batsa na yara ko duk wani abun ciki wanda ya saba wa doka da ta dace game da batsa na yara ko kayan lalata da yara, ko ƙarfafawa, adon, ko ba da shawara ga wasu don ƙirƙira ko raba irin wannan kayan;
- Wallafa ko fataucin abubuwan batsa waɗanda suka sabawa doka a ƙarƙashin doka; kuma
- Yin amfani da ayyukan ta hanyar da ba ta dace da doka ba.
- Shigar da Rugujewa da Amfani da Kayayyakin Ba bisa ƙa'ida ba
- Buga ko rarraba abun ciki wanda ya ƙunshi kowane ƙwayoyin cuta, malware, tsutsotsi, dawakai na Trojan, lambar ƙeta, ko wata na'urar da zata iya cutar da kayan aikin mu na fasaha ko tsarin ko na sauran masu amfani;
- Shiga cikin amfani da kai tsaye na Gidan Yanar Gizon Ayyuka waɗanda ke cin zarafi ko kawo cikas ga ayyukan, keta ƙa'idodin amfani da aka yarda da su idan akwai, ko kuma jama'ar Wikimedia ba su amince da su ba;
- Rushe ayyukan ta hanyar sanya nauyi mara nauyi akan API, Gidan Yanar Gizon Ayyuka ko cibiyoyin sadarwa ko sabar da aka haɗa da wani Gidan Yanar Gizon Aikin;
- Rushe ayyukan ta hanyar cusa kowane gidan yanar gizon Ayyukan tare da sadarwa ko wasu zirga-zirgar da ke nuna babu wata babbar niyya ta amfani da gidan yanar gizon Project don manufar da aka bayyana;
- Sanin shiga, ɓata, ko amfani da duk wuraren da ba na jama'a ba a cikin tsarin kwamfutar mu ba tare da izini ba; kuma
- Bincike, dubawa, ko gwada raunin kowane tsarin fasaha ko hanyoyin sadarwar mu sai dai idan duk waɗannan sharuɗɗa masu zuwa sun cika:
- Irin waɗannan ayyukan ba sa cin zarafi ko lalata tsarin fasahar mu ko hanyoyin sadarwar mu;
- Irin waɗannan ayyukan ba don riba ba ne (sai dai don ƙima don aikinku);
- kuna ba da rahoton duk wani lahani ga masu haɓakawa masu dacewa (ko gyara da kanku); kuma
- ba kwa yin irin waɗannan ayyukan da mugun nufi ko ɓarna.
- Wanda aka Biya don Bayar da Gudummawa ba tare da ya Sanar ba
- Dole ne ku sanar akan duk wanda ya dauke ku aiki, abokin aiki, wanda ke nufin biyanku ko wani tarayya dangane da kowanne irin gudummuwa ya kuka amsa, ko kuke tsammanin ku amsa, ko lada. Dole ne ku sanar a cikin daya daga cikin wadannan hanyoyin:
- bayani akan shafinku na masu amfani da shafukanmu
- bayani akan shafukanku na tattaunawa tare da kowanne irin nau’in gudummawa da za’a biya ku, ko kuma
- bayani a sashin tsokaci akan gyararraki dangane da kowanne irin nau’in biya don yin gyara.
- Bugu da kari, idan kun sanya bayani akan shafin yanar gizo wanda ba namu ba don tallatawa akan yin gyara a kan shafukan Wikipedia don amsan lada kowacce iri, dole ne ku bayyana duk wani asusu da zakuyi amfani da su don yin gyararrakin a kan shafin sadarwa na wancan kafar.
- Dokokin da ake iya amfani dasu, ko kuma dokoki da suka shafi wani Shafinmu da kuma Dokoki da Ka’idojin Gidauniyar, kamar wadanda suka shafi Rikici na Ra’ayi, ka iya kara iyakance gyara don karbae kudi ko kuma a bukaci karin bayanai. Misali, keta Dokokin Wikimedia (wanda akayi bayani a gaba a sashi na 6) don tallata gyara don amsar lada, cire bayanai ko kuma bayanai da suka gabata akan gyara don amsar lada, ko kuma fita daga shafin (log out) wanda zai sayya gano cikakken bayani aka gyara don karbae lada yayi wahala ya saba wa wannan sashin.
- Wata kungiyar al’ummar Wikimedia tana iya iya kirkirar wasu dokokin sanarwa na daban akan aikin gyara a Wikipeda na lada wadanda ka iya inganta ko kuma sauya wadannan dokokin, kuna iya bin wadannan dokoki a maimakon wadannan ka’idoji ma wannan sashin (mai take “Aikin Gyara don amsar kudi ba tare da Sanarwa ba”)
Don neman karin bayani, kuyi kokari ku karanta Tambayoyi da akafi yi akan bayani don gyararraki na amsar kudi.
Muna da damar wanzar da doka da kuma tilasta ta dangane da ka’idojin da aka zayyano a Sashi na 4 na wannan Ka’idojin Amfanin. A inda ta kama, tilasta bin wadannan ka’idoji na ita zama ta fuskar daukar matakai wanda ba’a lissafo ba a Gidauniyar Wikipedia Office Action Policy. Idan akwai bukatar tilasta bin wadannan dokoki a wata sabuwar siga, zamuyi kokari don sauya wadannan Dokoki na Matakan Ofishi akalla a cikin shekara daya (1) don shigar da sabon nau’in matakan.
- Watsa labaran Kamfanonin Kasuwanci
Rashin sanarwa akan gyararraki don karbae lada yana samar da nauyi mara dalili ga editoci masu bayar da gudummawa who investigate and enforce community policies. Don haka, dangane da take wadannan ka’idoji a wannan shafi akan rashin sanar da gyararraki don karbae kudi, kun amince da ku shigar zuwa ga “Med-Arb” (wata Kafar watsa labarai ce ta Kamfanonin Kasuwanci) kamar yadda aka sanar a sashi na 4 na wannan Ka’idojin Amfanin.
5. Tsaro da Lambobin sirri
Ku ke da alhakin kiyaye lambobinku na sirri da kuma sauran matakan tsaro, sannan kuma kada ku sake ku fadawa wani na waje.
6. Tambarin Kasuwanci
Duk da cewa kuna da ‘yancin mai yawa dangane da sake amfani da bayanai akan Shafukanmu na Yanar gizo, yana da muhimmanci cewa, a tsakanin Gidauniyar Wikimedia, da mu kare mutunci hakkokin tambarin kasuwancinmu (trademark) ta yadda zamu iya kare masu amfani da shafukan daga ‘yan danfara da ‘yan zamba. Saboda haka, muna bukatar ku da ku girmama tambarinmu. Dukkanin tamburan kasuwanci na Gidauniyar Wikimedia mallaki ne na Gidauniyar Wikimedia, sannan kuma dole ne duk wani amfani da sunan kasuwancinmu, tambarinmu, alamun huldodinmu, logo, ko kuma sunayen rukannanmu su kasance an bi dokokin Ka’idojin Amfani sannan kuma an bi dokarmu ta Dokar Tambarin Kasuwanci
7. Lasisin Bayanai
Domin haɓaka abubuwan gama gari na ilimin kyauta da al'adun 'yanci, duk masu amfani da ke ba da gudummawa ga Ayyuka ko Shafukan Yanar Gizo ana buƙatar su ba da izini mai yawa ga jama'a don sake rarrabawa da sake amfani da gudummawar su cikin 'yanci, muddin aka danganta wannan amfani da kyau kuma ana ba da wannan yancin sake amfani da sake rarrabawa ga kowane ayyukan da aka samu. Dangane da burin mu na samar da bayanai kyauta ga mafi yawan masu sauraro, muna buƙatar idan ya cancanta a ba da lasisin duk abin da aka ƙaddamar domin duk wanda zai iya samun damar yin amfani da shi kyauta.
Ka yarda ka bi lasisin a ka buƙata:
-
Rubutun da kuke riƙe da haƙƙin mallaka: Lokacin da kuka ƙaddamar da rubutu wanda kuke riƙe da haƙƙin mallaka, kun yarda da yin lasisi a ƙarƙashin:
- Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International (“CC BY-SA 4.0”), da
- GNU Lasisin Takaddun Kyauta na Kyauta ("GFDL") (ba a buɗe ba, ba tare da sashe daban-daban ba, rubutun gaba, ko rubutun baya).
(Masu sake amfani na iya biyan ko dai lasisi ko duka biyun.)
Iyakar abin da ke faruwa shine idan bugu na aikin ko fasalin yana buƙatar lasisi daban. A wannan yanayin, kun yarda da yin lasisi ga kowane rubutu da kuka ba da gudummawa a ƙarƙashin takamaiman lasisin da fitowar Aiki ko fasalin ya tsara.
Lura cewa waɗannan lasisin suna ba da izinin amfani da gudummawar ku na kasuwanci, muddin irin waɗannan amfanin sun dace da sharuɗɗan lasisi. Inda kuka mallaki Sui Generis Database Rights wanda CC BY-SA 4.0 ke rufewa, kun bar waɗannan haƙƙoƙin. A matsayin misali, wannan yana nufin gaskiyar da kuke ba da gudummawa ga ayyukan ana iya sake amfani da su cikin yanci ba tare da ƙima ba.
-
Sangare: Haɓaka muhimmin bangare ne na waɗannan lasisin. Muna la'akari da shi yana ba da daraja inda ya dace - ga marubuta kamar ku. Lokacin da kuke ba da gudummawar rubutu, kun yarda za a dangana ta cikin kowane salo mai zuwa:
- Ta hanyar hyperlink (inda ya dace) ko kuma URL zuwa mukala wacce kake so ka bayar da gudummawarka (tunda kowanne mukala na da shafin tarihi wanda ke lissafo duk wani wanda ya bayar da gudummawarsa ga mukalar, wanda suka kirkira da kuma editoci;~
- Ta hanyar mahadar hyperlink (inda ya kamata) ko kuma URL zuwa wani shafin, tsayayyen kwafi na yanar gizo, wanda ke da alaka da wasu lasisai, sannan kuma suna jinjinawa wanda ya kirkiri mukala daidai da iri wanda ake bayarwa wanda aka baiwa Shafin na Yanar Gizo; ki kuma
- Ta hanyar jerin daukakik masu kirkirar mukalai (amma ki sani cewa za a iya tace duk wani jerin sunayen wadanda ke kirkirar mukala don cire wadanda ke da kananan gyararraki ko kuma gyararrakin da basu da muhimmanci.
Kun amince cewa, idan kuka dauko rubutu a karkashin lasisin CC da ke bukatar inkayi, dole ne ku ambato sunan asalin marubuci(ta) a cikin salo mai ma’ana. Inda kuma wadannan ambato ke kasancewa acikin tarihin shafi (irin shafukan da aka kwafo daga wani shafi na Wikipeda), ya isar idan a ambaci mai rubutun a cikin tarihin gyararraki, wanda ake rikodin a cikin tarihin shafi, a yayin dauko rubutun. Sogar ambaton a wash lokutan suna kasancewa da tsananin dokoki a wasu lokutan (ba tare da alaka da lasisinsu ba), sannan kuna akwai lokutan da al’ummar Wikimedia zasu yanke shawarar cewa baza a iya amfani da rubutu da aka dauko kai tsaye ba saboda wasu dalilai.
Sake-Amfani: Mun yarda da kuyi amfani da bayanan da muke daukan nauyi, duk da cewa akwai iyakoki ga bayanai da aka bayar a karkashin “fair use” ko kuma makamain hakan a karkashin wasu kayadaddun dokokin hakkin kwafa. Dole ne kowanne bayani da kukayi amfani dashi ya zo daidai da lasisin.
A suk lokacin da kuka yi amfani ko kuma kuka yada shafin rubutu wanda al’ummar Wikimedia suka bunkasa, kun yarda ku zayyano asalin wanda ya kirkiri shafin a cikin daya daga cikin wadannan salo:
- Ta hanyar hyperlink (a inda ya dace) or kuma URL ko kuma shafukan da ba’a amfani da su (tunda kowanne shafi yana da shafin tarihi da ke jero sunayen daukakin wadanda suka bayar da gudummawa ga shafin, wanda suka kirkiri labarin da kuma editoci);
- Ta hanyar hyperlink (inda ya dace) ko kuma URL zuwa wani shafin, shafin yanar gizo da ake iya ziyarta kyauta, wanda ya dace da lasisin, kuma wanda ya ke jinjinawa masu kirkira a cikin yanayi da ke kwatankwaci da jinjina da ake baiwa Shafin yanar gizo; ko kuma
- Ta hanyar jerin daukakin sunayen masu wadanda suka kirkiri shafi (amma ku sani cewa za’a tace duk wani jerin sunayen masu kirkira don cire kananan gyararraki ko marasa muhimmanci).
Idan ya kasance cewa an dauko bayanan ne daga wata kafa, tana iya yiwuwa anyi wa bayanan lasisi ne a karkashin lasisin CC BY-SA amma ba GFDL ba (kamar yadda akayi bayani a sashin "Dauko Bayanai" da ke sama). A wannan yanayi, kun amince da cewa zaku bi ka'idojin lasisin CC BY-SA sannan baku da damar sake mata lasisi a karkashin GFDL. Don gano lasisin da yafi dacewa da bayanan da kuke so kuyi amfani da ita ko ku yada, ku duba rubutun da ke a kasan shafin, tarihin shafo, da kuma shafin tattaunawa.
Bugu da kari, ku lura cewa bayanai da suka samo asali daga shafukan waje kuma aka shigo dasu acikin shafukanmu zasu iya zama a karkashin lasisin da ke bukatar karin bayanai na ambato (citation). Masu amfani da shafi sun amince cewa zasu bayyana wadannan karin bayanai da ake bukata yadda ya kamata. Dangane da Shafukanmu, wadannan bukatu na iya kasancewa a matsayin banner ko kuma wasu alamu da ke nuna cewa wani sashi ko gabaki daya bayanan sun samo asali ne daga wani tushe. A inda akwai irin wadannan alamu karara, to suma masu amfani da shafi zasu karramasu.
Ga kowanne irin nau'in bayanan midiya wanda ba rubutu bane, kun amince zaku bi ka'idojin da suka shafi lasisi a karkashin inda aka samo bayanan (wanda za'a iya ganowa ta hanyar bude aikin da kuma duba sashin lasisin a sashin bayanan shafin ko kuma makamancin haka na shafin aikin). Yayin amfani da kowanne irin bayani da muke daukan nauyi, kun amince zaku bi ka'idoji da suka shafi wadannan bayanai da ake bukata kasancewa sun shafi lasisinsa ko fiye da hakan.
Yayin yin sauyi ko kuma karin bayanai ga kowanne midiya da kuka samo daga Shafukanmu na yanar gizo, kun amince zakuyilasisin sauye-sauye nan ko karin bayani nan dangane da lasisin da wannan bayani ke dashi tun daga farko.
Tare da bayanan dake rubuce da kuma na midiya, kun amince cewa zaku bayyana cewa an sauya ainihin aikin. Idan kuma kuna sake amfani da rubutun bayanan ne a wani shafin wikin, ya isar ku bayyana tarihin shafin cewa kunyi sauyi ga bayanan da kuka dauko. Ga kowacce kwafi ko kuma sauyayyun bayanai da kuka yada, kun amince zaku sanya lasisin lura wanda ke nuna a karkashin lasisin da aka saki bayanan, dangane da ko dai mahada (hyperlink) ko kuma URL na lasisin ina aka kwafo rubutun ko lasisin rubutun da kanta.
- Bincike akan amfaninku da Shafukanmu ko kuma sabis dinmu (a) don tabbatar da cewa keta dokar Ka’idar Amfani da Shafukanmu, dokar da suka shafi wani Shafi, ko kuma sauran dokoki da suka dace ya faru, ko kuma (b) don bin ka’idar duk wata doka da ta dace, tsarin shari’a, ko kuma wani bukata na gwamnati da ya dace;
- Gano, kiyayewa, ko kuma shawo kan matsalar wani magudi da ya faru, karya ko kuma zance mara tushe, tsaro, ko kuma matsalolin fasaha, ko kuma mayar da martani ga bukatun tallafawa masu amfani da shafukanmu.
- Sake amfani da shafi, sauya tsarin shafi, ko tsayar dasu, ko kuma sanya takunkumi ga samun damar bayar da gudummawa ga duk mai amfani da shafukanmu wanda ya keta dokar Ka’idar Amfani da shafukanmu;
- Haramta yin gyara ko bayar da gudummawa ko kuma toshe asusun mai amfani da shafi ko kuma damar isa ga wani ayyuka da suke bada damar keta dokar wadannan Ka’idojin Amfanin, wanda suka hada da cigaba da sanya abubuwan da basu dace da dokar ba a karkashin tsarin dokar da ta dace wanda suka dace da dokokin Hakkin Dan-Adam.
- Daukar matakan shari’a akan duk wani mai amfani da shafukanmu wanda ya keta wadannan Ka’idojin Amfanin (wanda ya hada da kai sammaci ta hukumomin doka; da kuma
- Kula da Shafukan na yanar gizo a cikin yanayi da zai tabbatar da amfani da su yadda suka dace sannan kuma a kare hakkokin, kayayyaki, da kuma kariyar kanmu da na masu amfani da shafukanmu, masu lasisi damu, abokan huldarmu, da kuma jama’a baki daya.
- Sulhu ta Kamfanin Midiya
8. Bin ka'idojin DMCA
Gidauniyar Wikipedia tana so ta tabbatar da cewa za’a iya amfani da bayanan da muke daukan nauyi ba tare da wata tsoron ka’idoji ba sannan kuma ba’a keta hakkokin mallakin wasu ba. Don yin adalci ga masu amfani da bayanan, da kuma wanda suka kirkira ko wanda ke da hakkin mallaka, dokar mu itace bin ka’idoji da suka dace da irin tsarin Digital Millennium Copyright Act (DMCA). Ta hanyar bin ka’idojib DMCA, zamu soke, a lokutan da suka dace, masu amfani da kuma wadanda ke da asusu a shafukanmu wadanda sun kasance masu yawa keta hakkokin mallaka ne akan Shafukanmu da Sabis dinmu.
Duk da haka, munyi la’akari da cewa ba kowanne korafi na soke aiki bane ya cancanta ko kuma akayi shi acikin kyakyawan ra’ayi. A irin wadannan lokutan, muna karfafawa masu amfani da shafukanmu da suma su mayarda martani a yayin da suka tabbatar da cewa sun bi soke ayyukansu ta hanyar ka’idojin DMCA bata dace ba ko anyi kuskure. Don karin bayani akan abun da zaku yi yayin da kuke tsammani cewa ba’ayi amfani da gargadin DMCA yadda ya dace ba, kuna iya tuntubar shafin yanar gizo na Lumen Database
Idan kai ke da mallakin bayanan da akayi amfani da su ba yadda suka dace ba a cikin daya daga cikin shafukanmu ba tare da izininka ba, kana iya neman a cire wannan bayani ta hanyar shigar da gargadi a karkashin DMCA. Don yin irin wannan sanarwa, ku taimaka ku tura mana sakon email a legal@wikimedia.org ko kuna snail mail our designated agent.
Ta wata hanyar kuma, zaku iya sanarwa ga al’ummominmu, wadanda suke kula da matsalolin hakkokin mallaka a cikin sauri da kuma daukan mataki fiye da yadda aka tsara a DMCA. A wannan yanayi, zaku iya daura gargadi kuna bayani akan matsalolinku na hakkin mallaka. Don matsaloli marasa girma ko kuma marasa izini na bayanai akan shafukanmu daban daban ku ziyarci shafin da ke dauke da matsalar keta hakkin mallakar. Kafin ku shigar sa kara ga DCMA, kuna kuma da damar tura sakon email a info@wikimedia.org.
9. Shafukan yanar gizo na waje da bayanansu
Kai ke da alhakin duk wani amfani da kayi da shafukan yanar gizo na waje ko kuma bayanansu. Duk da cewa, Shafukanmu da Shafukan yanar gizonmu na dauke da mahada zuwa shafukan waje da bayanansu, bamu tabbatar da kuma ba mu ke da alhaki ko nauyin samar dasu ba, gaskiyarsu, ko kuma makamantan hakan, kayayyaki ko kuma harkokinsu (wanda ya hada ba tare da iyakancewa ba, duk wata virus ko kuma wani abu da ka iya kawo cikas), ba kuma mu ke da alhakin kula da duk wani bayani daga wadannan shafuka na waje ba.
10. Kula da Shafukan Yanar gizo
Al’ummominmu ne ke da muhimmin alhakin gindaya ka’idoji da suka shafi Shaufakanmu daban daban da kuma tursasa su . A Gidauniyarmu ta Wikipedia, ba kasafai muke shiga al’amarin al’ummarmu ba wajen sanya dokoki da kuma tursasasu ba.
Zaku iya sanar damu akan bayanan da basu dace ba, ko kuma bayanai da sukayi karo da Ka’idojin Amfani da shafukanmu (wanda suka hada da kowacce ka’ida da kuma bayanai wanda aka hada acikin manazarta) don wasu dalilan ta hanyar tuntubarmu kai tsaye.
Kowanne Shafunmu yakan bayar da shafukan “Agaji” ko kuma “Kafar sadarwa” don neman karin bayani, ko kuma kayayyakin aiki daban daban na kai kuka. Ko kuma - idan kuna kokwanto - zaku iya tambayar membobin al’ummar mu don neman taimako, ta hanyr tura sakon email zuwa ga info@wikimedia.org ko kuma wani adreshi na wani harshe daga Sashin Amsan Koken Masu Gudummawa. Ku sani cewa wadannan asusun sakonni suna karkashin kulawar masu amfani da shafukanmu ne, ba Gidauniyar da kanta ba. A dalilin haka, kada a tuhumesu ko kuma a kai karansu don wasu bukatu.
Idan kuka kai isar da kukanku ga gidauniyar kai tsaye, zamu duba muga ta yadda tsare-tsaren al’ummominmu zasu taimaka wajen yin bincike a inda ya dace, ko kuma su magancesu.
A wasu lokutan, bukata ba iya tasowa, ko kuma kungiyar al’ummarmu su tuntubemu, don shawo kan matsala musamman edita mai bada matsala ko kuma bayanai marasa kyau a dalilin tsananin rudani a Shafinmu ko kuma halayya mai ban tsoro. A irin wadanan lokutan, muna da iko, ta yadda muka ga dana (ko inda ya dace da doka), mu yi:
Wadannan ka’idojin na Gidauniyar na iya faruwa ta hanyar software (kamar kariyar traffic flood (“kangewa daga sabis”)). A cikin irin wadannan lokutan mutane na iya sake bitarsu, upon request.
Acikin ra’ayin masu amfani da shafukanmu da kuma Shafukan da kansu, a cikin matsananci hali da aka haramtawa wani mai amfani da shafukanmu damar yin gyararraki a karkashin wannan sashin, an haramta masu kuwa sake kirkirar wani asusun ko kuma yin amfani da wani na daban ko kuma neman daman gyara wannan Shafi, face kuwa mun bada izini na musamman kan hakan. Ba tare da ka’idojin al’ummarmu ba, ita Gidauniyar da kanta ba zata haramtawa wani gyara amfani da shafukanta ba ko kuma ta kange su daga samun damar isa zuwa ga shafukanta ba kawai don suka da ake masa da kyakyawan zato sai dai don ya keta wadannan Ka’idojin Amfani da shafukan ko kuma dokokin al’ummominmu.
Gidauniyar Wikimedia da kuma membobinta har wayau na iya daukar mataki yayinda wani ya taka wadannan ka’idoji na al’ummarmu ko na Gidauniyar da kanta a wani Shafinmu wanda suka hada da kashedi, bincike, toshe damar gyara, haramta amfani sa shafi. Kun amince cewa zakuyi biyayya ga duk wani hukunci daga sashin sasancinmu wadanda kungiyoyin al’ummarmu suka kirkira dangane da Shafukanmu daban daban (kamar irinsu arbitrary committees); wadannan hukunce hukunce na iya hadawa da hukunci da ya dace da ka’idojin shafin da ya shafa.
Musamman masu yawan bada matsala wadanda aka dakatar da asusunsu kuma aka haramta masu ziyartar Shufaka daban daban za’a iya dakatar da su gabaki daya daga amfani da daukakin shafukanmu, dangane da tsarin Global Ban Policy. Dangane da tsarin Majalisar sasanci ko kuka wadannan Ka’idojin na Amfani, dokokinda mutane ke sanya su, wanda ya shafi wani Shafinmu ko kuma Shafuka da dama (kamar Dokar Haramci na Dukkanin Shafuka), kungiyar wata al’umma na iya sauya wadannan dokoki dangane da irin nasu tsare tsaren.
Tsayar da wani asusu ko kuma haramta ziyara ko kuma dakatar da wani mai amfani da shafukanmu a karkashin wadannan ka’idoji dole ne su zo daidai da dokar Sashi na 13 na wadannan Ka’idojin Amfanin.
Idan kuna gani cewa bamu jajirce wajen daukar mataki ba sosai akan roboton wani bayani mai matsala, ko kuma idan an zartar maka da hukunci a hukumar Gidauniyar wanda kake gani cewa kanaso kayi jayayya a kai, kana iya daukaka kara. Ana iya kara maka bayani akan sauran bayanai dangane da hanyoyin a wannan lokacin, ko kuma a sashin taimako na Shafin.
Muna da ikon dakatarwa (na wucin-gadi, ko kuma dundundun) akan yadda zamu dauki matsaya akan rahotanni ko kuma sauran bukatu daga masu amfani da shafukanmu ko kuma sauran kungiyoyin waje, ko akan wani bayani wanda aka take doka ko kuma wasu bayanai da ka iya haifar da matsaloli ko kuma wani aiki, idan anyi wadannan abubuwan da mummunan nufi, akai ta maimaita su, ba tare da dalili ba, da/ko kuma don a ci zarafin wani. A yanayin da ya dace, zamu goge adireshin ka na email daga tsarin adiresoshinmu, sannan kuma zaka iya riskarmu ne kadai ta adireshin fostal dinmu idan kana bukatar yin karin tattaunawa tare da mu a yayin da aka haramta maka amfani da shafukanmu. Dangane da kananan matsaloli kuwa (misali, an kai akalla korafe-korafe guda uku a cikin mutunci dangane da wani korafi mara tsanani), wannan dakatarwa na iya zama na wucin-gadi. Yawan maimaita ko kuma yawan maganganu na cin zarafi ka iya jawo matakai na dundundun.
11. Sansanci da Dokokin Shafuka
Majalisar Amintattu na Gidauniyar Wikimedia tana sakin dokoki a hukumance daga lokaci zuwa lokaci. Wasu daga cikin wadannan dokokin ka iya zama wajibi ga wasu Shafukanmu, sannan kuma, a yayin da suka zamo hakan. kun amince cewa zaku bi su a aikace.
12. Dokokin API
Mun samar da wasu jerin API, wadanda suka hada da na shigar da bayanai da kayan aiki makamantansu, don ba wa masu amfani da shafukanmu damar gina abubuwa da zasu bunkasa yada ilimi kyauta. Yayin amfani da API din, kun amince zaku bi duk wasu dokoki da shuka jibanci amfani da wadannan APIs din, wanda suka hada da amma ba su kenan ba Dokar masu amfani da shafi da kuma hukuma,Dokar Robot, da kuma API:Etiquette (a hade, sune “API Documentation”), wadanda aka hade su acikin wadannan dokokin amfanin ta hanyar manazarta.
13. Kawo karshe
Duk da cewa muna fatan cewa zaku tsaya ku cigaba da bayar da gudummawarku ga wadannan Shafukan, kuna iya daina amfani da sabis dinmu a kowanne lokaci. A wasu lokutan (muna fatan han bazai faru ba) tana iya zama wajibi ga ko dai garemu ko kuma kungiyoyin al'ummar Wikipedia da membobinta (kamar yadda aka tsara a Sashi na 10) da mu kawo karshe sashi ko kuma daukakin sabis dinmu, mu kawo karshen wannan Ka'idojin Amfanin, mu dakatar da asusun ka/ki ko kuma damar isa shiga shafukanmu, ko kuma mu dakatar da kai/ke a matsayin mai amfani da shafukanmu. Idan an dakatar da asusun ka ko kuma an haramta maka shiga shafukanmu saboda wani dalili, hakan ba zai shafi gudummawowin da ka bada da kuma tarihin abubuwan da ka yi dangane da (wanda ya hada da duk wani sako da ka tura mana), kuma sannan kana iya ziyartar shafukanmu na al'umma kawai don karatun bayanan da suke bayyane ga al'umma a Shafukanmu. A cikin irin wadannan lokutan, duk da haka, ba za ka iya riskar asusunka ba ko kuma gyare-gyare. Ko yaya, ko ba tare da take wadannan Ka'idojin Amfanin ba, muna iya dakatar da kai, tare da ko kuma ba tare da wani sila ba, sannan kuma tare da ko kuma ba tare da gargadi ba. Ko da ace kuwa bayan an dakatar da kai wajen amfani ko kuma bayar da gudummawa, ko an haramta maka shiga ko kuma an baka hutu na dan lokaci, wadannan Ka'idojin Amfanin zasu cigaba da wanzuwa dangane da irin wadannan dokoki, wanda suka hada da na Sashi na 1, 3, 4, 6, 7, 9-16, da kuma na 18.
14. Jayayya da kuma Hurumi
‘’An jaddada don nuna muhimmanci’’
Muna fatan cewa babu wata babban matsala da zata taso wacce ta hada da kai/ke, amma, idan ya zamana an sama sabani, muna baku shawarar da ku nemi sasanci ta hanyar sansanci da Shafukan Gidauniyar Wikipedia ta tanada ko makamantansu. Idan kunyi niyyar kai mu kara don shari'a, kun amince cewa zaku kai kara ne kuma ayi shawo kan matsalar a kowanne kotu na jiha ko kuma na tarayya wanda ke a birnin San Fransisci County, California. Har wayau, kun kuma amince cewa dokokin jihar California sannan kuma, duk inda matakai suka kai, cewa dokokin Kasar Amurka zasu jagoranci wadannan Ka'idojin Amfanin, da kuma duk wata doka ta shari'a da zata taso a tsakaninmu da ku (ba tare da la'akari da dokokin ka'idojin rikici ba). Kun amince cewa zaku sallamar da duk wata hurumi na son kai, kuma kun amince cewa wurin shari'ar ya dace, a kotunan da ke zaune a San Fransisco County, California, game da duk wani mataki ko kara da ta shafe mu ko kuma wadannan Ka'idojin Amfanin.
Don tabbatar da cewa an shawo kan matsaloli tun lokacin da suka taso, kun amince cewa ba tare da la'akari da dyj wani matsayi ko doka da ta bambanta da wannan ba, duk wani ikirari ko kuma wasu matsaloli da suka taso a wajen ko kuma da suka shafi amfani da sabis dinmu ko wadannan Ka'idoji na Amfani dole ne a kai kararsu a karkashin ka'idojin da suka dace na iyakoki ko kuma, idan da wuri ne, shekara (1) daya bayan samun hujjoji da suka shafi wadannan ikirari ko kuma matsala da aka gano ta hanyoyin da suka dace (ko kuma a kulle har abada).
Kamar yadda aka yi bayani a sashi na 4 na wadannan Ka'idojin Amfanin, kun amince cewa zaku sasanta matsalar Gyara don amsar Kudi ba tare da an Fallasa ba a Kafafen Midiya na Sulhu kamar yadda Gidauniyar ta tanada. Kamfanonin Sulhu na Midiya sun kasance kafar shari'a inda, a karshen tsakiyar ko kuma karshen rana, duk wasu rikice-rikice da ba'a shawo kansu ba, zasu zamo cewa masu sulhu ne zasu tattauna akansa a kowanne a cikin tsarin doka ta shari'a. Zasu faru ne kuma a ganawa ta hanyar taro ta wayar hannu ko kuma taro na bidiyo. Idan ana bukatar taro na kai tsaye, to wannan Kamfanin Kasuwanci ta Midiya zata faru nw a birnin San Fransisco, Carlifornia. Wadanda shari'ar ta shafa zasu raba duk wata asara ta kudi da za'a kashe wanda suka shafi sulhu/sansanci dai dai a tsakaninsu.
Kun amince, a matsayin wani sashe na Kamfanin Sulhu, don bada hadin kai ga Gidauniyar, wanda suka da samar da bayanai akan lokaci wanda kake da su dangane da rashin sanar da cewa an biya ka don yin wani gyara wanda ya hada da asusun da kayi amfani da shi, mukalai da suka shafa, da kuma abokan hulda wanda suka biya kudin aikin.
Kamfanonin Sulhu na Kasuwanci suna da alaka da kuma suna karkashin Federal Arbitration Act zuwa wani matsayi da masu sulhu kan zamo masu sasanci. Dayan sashin na shari’a zasu iya amsar kudin da aka biya mai shari’a (wanda suka hada da duk wani kudi da aka biya wanda suka shafi Kamfanin Sulhun da kuma tursasa bin dokokin) da kuma duk wani kudi ya shafi bincike da tursasawa akan hakkokin ta. Wani sashi na iya zama “mai rinjaye” ko da kuwa basu yi nasara a kowanne bangare na shari’ar ba.
Idan kuma akan wani dalili an samu gabaki daya wannan Kamfani na Sulhu an same sun zamo wadanda baza’a iya tilasta su ba, kun amince cewa zaku kawo karshen duk wata rikici kamar yadda akayi bayani a farkon wannan sashi.
15. Tsame-hannu
An jaddada don nuna muhimmancinsu
A Gidauniyar Wikimedia, muna yin iya kokarinmu don samar da bayanai na ilimi da kuma tunatarwa zuwa ga al’ummomi daban daban, amma amfaninka da sabis dinmu suna akan gangancin ka ne. Muna sakin wadannan bayanai ne “kamar yadda suke” kuma “yadda aka samar da su”, sannan kuma mun tsame hannunmu daga duk wata tabbaci ko makamancin hakan, don cancantarsu don wani abu, ko kuma rashin keta hakkin mallaka. Bamu bada wata tabbaci ba akan ko cewa sabis dinmu zasu biya muku bukatunku, ko kuma zasu zama daidai, amintattu, ba tare da tangarda ba, akan lokaci, daidai, ko kuma rashin kuskure, ko kuma cewa bayananku zasu zamo amintattu.
Bamu da wata alaka da bayanai, data, ko kuma ayyukan sauran mutane, kuma ba zaku kama mu ba, ko darektocinmu, ko jami’un mu, ko ma’aikatan mu, ko kuma wakilan mu, daga duk wani nauyi ko kuma duk wata barna, wanda aka sani da wanda ba’a sani ba, wanda suke tasowa ko kuma a duk wata alaka na ikirari da kuke da shi sauran mutane na waje. Babu wata shawara ko kuma bayani, ko da kuwa a rubuce ko kuma ta baka, wanda aka samo daga gare mu ko kuma ta hanyar sabis dinmu ba su bada wani tabbaci na akasin abinda aka gindayo a cikin Ka’idojin Amfaninmu.
Duk wani bayani wanda aka dauko ko kuma aka samo ta hanyar amfani da sabis dinmu sun faru ne akan dalilin amincewar ku da kuma gangancin ku, kuma ku kadai zaku zama masu alaka da nauyin da ya shafi barna daga na’urar komputa ko kuma asarar bayanai a dalilin dauko bayanai ko makamancin haka. Kun amince cewa baki da wata iko ko nauyi akan goge wani bayani, ko kuma gazawa wajen ajiye bayanai ko kuma sarrafa su, duk wasu bayanai ko kuma tattaunawa da sabis dinmu ke kula da su. Muna da ikon mu sanya iyakoki akan yadda za’a yi amfani ko kuma ajiye bayanai ta yadda muke so a kowanne lokaci tare da ko ba tare da sanar da ku ba.
Wasu kasashe ko kuma hurumin shari’a basu amincewa sa irin wadannan ka’idojin tsame-hannu ba, saboda haka zasu iya shafar ku ko dai ta wani bangare ko kuma gabaki daya dangane da tsarin dokar ku.
16. Iyakoki akan Nauyi
An jaddada su don nuna muhimmanci
Gidauniyar Wikimedia ba zata dauki wani nauyi ko kuwa na wani bangare don wani abu da ya faru ko dai kai tsaye, ko ba kai tsaye ba, ko kwatsam, ko na musamman, ko a dalilin wani abu, ko kuma wata barna, wanda suka hada amma ba su kadi ba da, barna na asarar riba, zumunci, amfani, data, ko asarar kayan amfani, ko da kuwa an sanar damu akan yiwuwar faruwar wannan barna. Babu wani yanayi da zai sa kudin da zamu biya ya wuce dalar Amurka dubu daya (USD 1000.00) gaba daya. A cikin yanayin da irin wadannan dokoki ka iya hana wadannan iyakoki ko kuma cire wadannan nauyi, ko tsautsayi, ko kuma sakamakon wani barna, wadancan iyakoki ko ka’idoji ba zasuyi aiki akan ku ba, duk da cewa nauyin da zamu dauka zai kasance mai matukar iyaka dangane da ka’idar da doka ta tsara.
17. Sauyi ga wadannan Ka’idojin Amfanin
Kamar yadda shigar da bayanai da al’ummar Wikimedia ke yi a cikin Shafukanmu ke da muhimmanci a wajen bunkasa da kuma cigaban shafukan, munyi imani da cewa shigar da bayanai daga al’umma acikin wadannan Ka’idojin Amfani na da muhimmanci don cigaba da kyautatawa masu amfani da shafukanmu yadda ya dace. Har wayau suna da muhimmaci a wajen tabbatar da harkalla na adalci. Saboda haka, zamu samar da wadannan Ka’idojin Amfanin, da kuma damar sake yin bitar mau sosai a nan gaba ga wadannan Ka’idojin Amfanin, don samun tsokacin al’umma na akalla tsawon kwanaki 30 kafin a kare yin tsokacin. Idan aka samu wani tsokaci da ya zamana mai amfani, zamu kara bayar da tsawon kwanaki 30 don sake yin tsokaci kafin a fassara zuwa akalla harsuna guda uku (wanda muka ga damar zaba) sannan a yada su. Zamu karawa mutane karfin gwiwar fassara wannan tsokaci da aka bayar zuwa ga yaruka daban daban da suka dace. Dangane da sauye sauye da suka shafi doka ko gudanarwa, ko gyaran wata magana mai kuskure, ko kuma sauye sauye dangane da tsokacin mutane, zamu bayar da sanarwa na akalla kwanaki uku (3).
Saboda tana iya kamawa mu sauya wadannan Ka’idojin Amfanin, zamu bayar da sanarwa akan wadannan sauye sauye da kuma damar yin tsokaci ta Shafinmu na yanar gizo, da kuma ta hanyar sanarwa ta WikimediaAnnounce-L. Duk da haka, muna bukatar ku da rinka duba sabbin sauyi akan wadannan Ka’idojin Amfanin. Cigaba da amfani da sabis dinmu bayan shigar da sabbin Ka’idojin Amfanin a cikin tsari zai biyo bayan bita da amincewa da wadannan Ka’idojin Amfani daga wajen ku. Don kariya ga Gidauniyar Wikimedia da kuma sauran masu amfani da shafukanmu irin ku, idan baku amince da wadannan Ka’idojin Amfanin namu ba, ba za ku iya amfani da sabis dinmu ba.
18. Wasu Ka’idojin
Wadannan Ka’idojin Amfanin ba suna nufin akwai hakkin aiki, hukuma, abota, kula na hadin kai ko kasuwancin hadin gwiwa a tsakanin ku da mu Gidauniyar Wikimedia ba. A dalilin dokoki irinsu European Economic Area law, United Kingdom law, da dai sauran dokoki wanda suke da alaka da irin wannan tsarin, ba wai kuna aiki ne ba “a karkashin ikon” Gidauniyar ne ba yayin da kayi amfani da sabis dinmu. Idan kun sanya hannu akan wata yarjejeniya ta daban a tare da mu, wadannan Ka’idojin Amfanin sun ta’llaka ne gaba daya a tsakanin ka da mu. Idan akwai wani rudani a tsakanin wadannan Ka’idojin Amfanin da kuma rubutacciyar alkawari a tsakanin ka da mu, wannan yarjejeniya da aka rattaba hannu zai wanzu.
Kun amince cewa muna iya baku sanarwa, musamman wanda suka shafi sauyi akan Ka’idojin Amfani, ta email, sakon email a kai da kai, ko kuma daurawa akan Shafukanmu ko Shafukan Yanar gizo.
Idan a wani yanayi, bamu wanzar da ko kuma tursasa wadannan Ka’idojin Amfanin ba, ba wai yana nufin an kore su bane.
Kun fahimce cewa, face mun amince bane a rubuce, ba ku da wani bukata da biyan kudi akan wani aiki, gudummawa, ko shawara da kuka ba mu, al’ummar mu, ko kuma Shafukan Wikimedia ko kuma sauran Shafukanmu.
Ko yaya duk wani aiki wanda ke daban da wadannan Ka’idojin Amfani, mu (Gidauniyar Wikimedia) da kuma ku kun amince cewa bazaku sauya ka’idojin da bukatu na lasisin kyauta da aka gina a wadannan Shafuka ba ko kuma sauran Shafukanmu a yayin da wadannan Ka’idojin Amfani suka bayar da damar sakin wannan lasisin kyauta.
An rubuta wadannan Ka’idojin Amfanin ne a harshen Turancin (Amurka). A yayin da muke fatan fassarar wadannan Ka’idoji su zamo daidai, a yanayi na bambancin ma’ana a tsakanin ainihin bugun na Turanci da wanda aka fassara, bugun ainihi na Turancin za’a yi amfani da shi.
Idan an sami wani ka’ida ko kuma wani sashi na Ka’idojin Amfanin sun taka doka, babu ma’ana, ko kuma baza’a iya tilasta su ba, wanda doka ko bangaren wannan zai zama daban da sauran wadannan Ka’idojin Amfanin kuma za’a yi kokarin tilasta su iya gwargwadon da iko ya bayar, sannan kuma duk wani sauran ka’idoji na wadannan Ka’idojin Amfanin zasu kasance ana tilasta amfani da su da karfin gaske.
Mun Gode!
Muna godiya da daukan lokaci da kukayi don karanta wadannan Ka’idojin Amfanin, kuma sannan muna matukar farin ciki da samun ku a matsayin masu bayar da gudunmuwa ga Shafukanmu da kuma amfani da sabis dinmu. Ta hanyar gudummawar ku, kuna taimakawa wajen gina wani abu mai girman gaske - ba wai kawai tarin muhimman bayanai na Shafuka wanda aka gyara acikin hadin kai wanda ke samar da ilimi da bayanai ga miliyoyi wadanda in ba haka ba bazasu sami damar isa gare su ba, amma har da tsayayyun mutane masu tunani iri daya da kuma sauran abokn hulda, wanda suka mayar da hankali don cimma wani buri na karamci.