Kwamitin Ombuds / 2019 / CU Tsarin Duniya kan bayyana bayanai
About the commission — Make a report — Email the commission — Discuss the commission | |
Activity reports: 2024 • 2023 • 2022 • Earlier Published decisions |
Wannan shi ne kwafin jama'a na shawarar da Hukumar Ombuds ta yanke wanda aka buga a watan Satumbar 2019. |
Tushe
Kwamitin Ombudsman sun tura sakon emel ga dukkannin Masu duba Editoci (CheckUsers) da su fayyace sosai a wani irin al'amari ne Masu duba Editoci zasu iya bayyana bayanai da suka tattara daga matakinsu na musamman a matsayin Masu duba Editoci. A kasa akwai rufaffen kwafi na emel din. Wannan ba wai doka bace, ba kuma zata kawo kowanne irin canji bane ga bayanan da suke nan tun tuni, kawai dai karin haske ne akan Dokan Samun bayanai na sirri, da Dokar Sirri, da kuma Dokan Duba Editoci.
Bayanai
Kwamitin Ombud sun gano cewa a yayin da Amfani da fitar da bayanan da basu shafi 'yan waje ba abubuwan da suke da karancin dacewa a fitar da su, mun fahimci cewa §(b)(v) ba'a gane su a harkokin yau da kullum da kayan aikin Masu duba Editoci na kowanne furojet, musamman a yarukan da ba Turanci ba.
Kwamitin Ombuds sun kirkiri wannan takarda ne don sanar da cewa musamman abun da suka fi dacewa a bayyana, da kuma abubuwan da bai kamata a bayyana su ba. Idan kwamitin Ombuds suka samu korafin da bai bi ka'idojin da aka lissafo ba a nan, to za'a bukaci su bayyana matsalar ga Majalisar WMF, su bukaci daukan mataki akan Mai duba tantancewa.
Ƙa'idojin bayyana bayanan mai binciken:
- Wajibi ne duk wani bayyana bayani ya zamo don kaucewa ƙarin barna ga shafi.
- Inda ake buƙatan bayyana bayani don are shafi (kamar kangewa, kare shafuka, ko korewa), dole ne ya zamana babu wani wanda ke da isa ga irin wannan bayani da keke da shi yadda zaka fitar da bayanin a lokacin da ya dace (Misali: mai binciken ptwiki da yake bukatan bayyana adireshin IP na wani daga arwiki da yake so wani mai kula daga arwiki ya kange daga yin gyara. Idan arwiki tana da masu duba shaafukanta, ko wakilai suna kusa da zasu iya wanzar da aikin, to kana iya fada musu a maimako)
- Dole ya zamana ace bakada ra'ayin son kai a ciki, ko kuma alamun son kai da al'amarin ko kuma editan da ya shafa (Misali: Ba zaka shiga rikici da editan ba). Mu sani cewa kawai don ka dauki matakin gudanarwa a kan edita ba wai yana nufin kana da ra'ayin son kai bane.
- Bayyana mafi ƙarancin bayanai masu yiwuwa (Misali: idan ana buƙatar bayyana wuri, kada ku ba da adireshin IP, ba da wuri mai faɗi)
- Wajibi ne kowanne bayyanawa ya zamo ba a sararin jama'a ba, sai dai kawai a inda 'yan tsirarun editoci zasu iya ganin bayanan, don iyakance fitar da bayanai iya gwargwado. Misalan wuraren da suka dace sun hada da: Tura sakon emel zuwa wani edita, ko kuma ta Special:EmailUser zuwa wani edita. Misalan wuraren da basu dace ba sun hada da: Sanarwa akan shafukan wiki, turawa zuwa tashohin jama'a a IRC, da kuma turawa ta jerin masu ganin emel.
A madadin Kwamitin Ombuds, -- Amanda (aka DQ) 13:21, 3 September 2019 (UTC)
Matsalolin Fassara
Duk wata fassara da taci karo da fassaran harshen-Turanci, za a dauki na fassaran harshen-Turancin a matsayin majagaba.