Tsarin Dokan Tafiyar/Kwamitin yin daftari/Sanarwa - An buɗe kuri'un rattabawa
Zaɓuɓɓuka don tabbatar da Tsarin Dokan Tafiyar Wikimedia yanzu ta buɗe - jefa kuri'ar ku
- Kuna iya samun wannan sakon da aka fassara zuwa ƙarin harsuna akan Meta-wiki. Please help translate to your language
Barka kowa da kowa,
Zaɓuɓɓuka don tabbatar da Tsarin Dokan Tafiyar Wikimedia yanzu ta buɗe. Tsarin Dokan Tafiyar Wikimedia takarda ce da aka tsara don ayyana ayyuka da nauyi ga duk membobi da ƙungiyoyin tafiyar Wikimedia, gami da ƙirƙirar sabuwar hukuma - Majalisar Duniya - don shugabancin tafiyar.
Ana samun sigar ƙarshe ta Tsarin Dokan Tafiyar Wikimedia akan Meta a cikin yaruka daban-daban.
Za a fara kada kuri'a a SecurePoll a ranar 25 ga Yuni, 2024 da karfe 00:01 UTC kuma za a kammala ranar 9 ga Yuli, 2024 da karfe 23:59 UTC. Da fatan za a karanta ƙarin akan bayanan masu jefa kuri'a da sauran cikakkun bayanai.
Bayan karanta Kundi, don Allah zabe a nan kuma raba wannan bayanin.
Idan kuna da wasu tambayoyi game da ƙuri'ar rattabawa, tuntuɓi Hukumar Zabe ta Kundi ta cec@wikimedia.org.
A madadin CEC,