Jump to content

Wikimedia Foundation elections/2021/2021-08-18/2021 Voting Opens/ha

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Wikimedia Foundation elections/2021/2021-08-18/2021 Voting Opens and the translation is 100% complete.

Kaɗa ƙuri'u na Zaɓen Kwamitin Amintattu na 2021 an fara yanzu. Ƴan'takara na al'umma an tuntuɓe su da su sanar da neman takarar su. Bayan makonni uku masu tsawo na kira ga ƴan'takara, akwai ƴan'takara 19 dake neman a zaɓe su a 2021.

Kwamitin Amintattu na Wikimedia suke lura da ayyukan da Gidauniyar Wikimedia take yi. Kwamitin na son inganta ƙwarewarsu da banbance banbancensu amatsayin ƙungiya. Sun raba ɓangarorin ƙwarewa waɗanda suke saran samun su daga sabbin amintattun.

Wikimedia movement na da damar zaɓen ƴan'takara da suke da inganci da zasu iya samar da buƙatun tafiyarsu na wasu shekaru masu zuwa. Kwamitin na saran zaɓar huɗu da akafi baiwa ƙuri'u da su kasance daga cikin amintattun. Zagayen aikinsu zai fara a Satumba kuma zai ƙare a shekaru uku masu zuwa. Samu ƙarin bayani akan Kwamitin Amintattun a gajeren bidiyo ɗin nan.

Kaɗa ƙuri'a ayanzu har zuwa Augusta 31.

A ƙasa wasu muhimman bayanai ne akan yadda za'a gudanar da zaɓen.

Samu ƙarin bayani game da ƴan'takarar

Ƴan'takara daga cikin tafiyar mu sun miƙa buƙatar neman takararsu. Samu ƙarin bayani game da kowane ɗan'takara dan sanin wanda ya dace ku zaɓa. Al'umma na Wikimedia sun miƙa tambayoyi ga ƴan'takaran dan su amsa a lokacin yin kamfe. Ƴan'takaran sun bayar da amsoshin tambayoyin da akayi masu inda Kwamitin Zaɓe suka tattara a Meta.

Zaɓe

Kaɗa ƙuri'a a Zaɓen Kwamitin Amintattu na 2021 an fara ne a 18 Augusta 2021 kuma za'a kulle a 31 Augusta 2021. Ƴan Kwamitin zabe zasu zaɓi Tilon ƙuri'a da aka bayar ga kowane ɗan takara a tsarin gudanar da zaɓen. Masu kaɗa ƙuri'a zasu iya jera zaɓin su akan matsayi. Samu ƙarin bayani akan cancantan yin zaɓe, yadda ake kaɗa ƙuri'a, da Tambayoyin da aka fiye yi akan kaɗa ƙuri'ar.

Taimaka wurin ganin an zaɓi mutane da suka fi cancantan kasantuwa a tafiyarmu a wannan lokaci. Zaɓa kuma ku yaɗa wannan, saboda mutane sosai suyi zaɓen. Waɗanda aka zaɓa zasu taimakawa Gidauniyar Wikimedia kuma su tallafa akan buƙatun tafiyarmu na tsawon shekaru masu zo.

Da Kyau,

Kwamitin Zaɓe