Jump to content

WWC2023/Sukolaship

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page WWC2023/Scholarship and the translation is 94% complete.

Za a gudanar da taro na uku na WikiWomenCamp a New Delhi, Indiya, daga ranar 20 zuwa ranar 22, Oktoba 2023. Kasance tare da mu don samun gogewa da Kuma samun cigaba. Taron kuma zai mai da hankali kan haɓaka, jagoranci, da haɗin kai. Taken taron na bana shi ne "Taswirori, Tashi," yana mai da hankali kan karfafa mata da kuma shawo kan matsalolin al'umma.

Menene ma’anar sukolaship?

Wannan wani tallafi ne na kudi wanda ake baiwa mutane don maye kudaden da ake bukata wajen halartar taron. Makasudin wannan tallafi na sansanin mata shine samar da daidaiton dama danagane da harkokin sansani da kuma fa’idantuwa daga ilimomi na musamman, koyarwa, da kuma cigaban juna da wannan sansani zai bayar.

Rukunai

Tare da niyyar tabbatar da ingantaccen aiwatarwa da haɓaka tasirin shirin, shirin sansanin Mata (women camp) ya kasu kashi biyu- Dabaru da Ƙarfafa ƙarfi.

Jigo guda biyu, dabarun da haɓaka iya aiki, za su ba da damar mayar da hankali da cikakkiyar hanya. Taken dabarun zai jaddada hangen nesa, tsare-tsare, da sa hannun masu ruwa da tsaki, yayin da jigon samar da iya aiki zai mayar da hankali kan inganta kwarewa, albarkatu, da dorewa.

Hakanan an raba kujerun tallafin karatu zuwa kashi biyu, bin tsarin guda ɗaya inda An n tanadu 25 don dabarun yayin da aka tanadi 35 don haɓaka.

Gaba ɗaya an tranadi kujeru 45 don ƙasa da ƙasa da kuma wasu 15 don mahalarta na yankuna.

Abubuwan fata daga mai karɓar tallafin karatu

  • Halarci zaman taro na watan Agusta da Satumba
  • Bayanin yau da kullun a tare da Camp Buddy
  • Shiga cikin binciken (s) (bayan sansanin)
  • Shiga cikin tarurrukan dabaru na lokaci-lokaci (Kungiyar Dabaru)
  • Aiwatar da ƙwarewar da aka samu (Ƙungiyoyin Haɓaka Ƙarfafa)

Abin da tallafin karatu ya kunsa

  • Tafiya zuwa taro da kuma komawa bayan an kammala taron
  • masauki da abinci a cikin kwanakin taron
  • Kudin Visa

Muhimman Lokuta

Jadawalin lokacin da ake tsammani don Shirin taron WikiWomenCamp 2023 shine kamar haka:

  • Kwanan watan fitar da fom na bayar da tallafin karatu: 13 Yuni 2023
  • Kwanan rufe takardar neman karatu: 4 Yuli 2023
  • Sanarwa sakamakon: tsakiyar Yuli 2023

Nema

Domin nema, da fatan za a cika wannan fom.

Applications have closed.