Jump to content

China-Nigeria Wiki Collaboration/Hausa

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki


Babban shafiDokokiMukaloli - NajeriyaMukaloli - China
English中文YorubaIgboHausa

Haɗingwiwar China-Najeriya ta Wiki

rightFlag of the People's Republic of China Flag of Federal Republic of Nigeria
Haɗingwiwar China-Najeriya ta Wiki, frojet ce wanda haɗin kai ne na farko, tsakanin Wikimedia UG Nigeria (WUGN) da Wikimedians of Mainland China (WMC) zasu jagoranta da zimmar cimma ƙarin ƙarfafa ƙawance tsakanin ƙungiyoyin biyu dan rubuta muƙalu masu matuƙar inganci akan tarihi, al'ada, taswira, cigaba, tarihin mutane, da sauran batutuwan da ba za'a rasa ba.

Frojet ɗin 1st (farko) a wannan haɗakar zai fara ne daga Augusta 1st, 2021, sannan zai cigaba da gudana har zuwa Augusta 31st, 2021. Masu taimako daga dukkanin al'ummun biyu ne zasu riƙa rubuta muƙalu akan kowannen su.

1st Frojet (Dokoki)

A taƙaice: Dan ƙirƙira ko fassara muƙalu da suka danganci batutuwan Najeriya (dan Chinese) da China (dan Najeriya), tare da manazartoci masu kyau da inganci, daga tsakanin Augusta 1st - Augusta 31st, 2021 UTC.

  • Maƙala dole ta zama tana da dangantaka da Najeriya (dan Chinese) da kuma China (dan Najeriya).
  • Muƙalar ta zama anyi ta ne tsakanin Augusta 1st - Augusta 31st, 2021 (UTC).
  • Muƙalar ta cimma ingancin gasar; kamar yadda aka bayyana akan kowane harshen da za'a yi gasar akai. (exclude Infobox, template etc.)
  • Muƙalar dole tazama tana da ingatattun manazartu; bayanan dake da shakku ko cece-kuce acikin muƙalar dole a tabbatar dashi ta hanyar bada nassi mai inganci kuma a sanya a maƙalar.
  • Muƙalar kada ta zama kawai dukkaninta fassarar inji/mashin ne, fassarar ta zama dukkaninta wanda ya rubuta ta ya duba ta gaba da baya kuma anyi gyararrakin da suke ciki duka.
  • Kada a samu wani matsala da muƙala. (no copyright violations, questions of notability, etc.)
  • Muƙalar dole ta zama mai bada bayani akan abinda take magana ko aka rubuta dan shi.
  • Duk muƙalar da organizers suka kirkira dole wasu organizers din ne zasu duba.
  • Alƙalai daga al'ummar Sin/Najeriya sune zasu tabbatar ko muƙalar ta can-canta ko kuma bata can-canta ba ga manhajar Wikipedia ɗin da aka yi ta.
  • Duk masu shiga gasar da suka kirkiri a kalla maƙala ɗaya zasu sami kyautar barnstar bayan kammala gasar edit-a-thon ɗin.

Al'ummu