Sake sunan amfani
Sunan masu amfani da ayyukan Wikimedia suka zaɓa da kansu ba a daskare su ba ma'ana za'a iya sauya su. Kowane stewad ko masu sauya suna na duniya zai iya canza sunan mai amfani. Za a iya canza maka suna zuwa sunan da kake so kuma wanda babu shi. Tuntuɓi kowane mai canza suna na duniya kuma nemi umarni.
Kuna iya ajiye buƙatar canza sunan mai amfani a Buƙatun Steward/Ana canza sunan mai amfani.
Yadda ake sauya suna
- Kada ka nemi sauya suna a wannan shafin
- Kada ka ƙirƙi sabon account da sunan da kake so ka sauya
Saka nema a Special:Sake suna na bai ɗaya, ko a Steward requests/Sauya sunan mai amfani.
Yadda yake aiyuka
Akan buƙatu, masu kula ko masu sake suna na duniya na iya canza saitunan asusun mai amfani da tarihin labarin kamar yadda duk gyare-gyaren da aka yi a baya na mai amfani ana danganta shi da sabon suna. Anyi hakan sau da yawa a baya, ko dai da son rai, ko kuma tilastawa bisa ga manufofin masu amfani da muggan laifuka akan Wikipedia na Ingilishi. Goge asusu ba a aiwatar da shi akan ayyukan Wikimedia, don haka idan kuna son ɓoye suna bayan yin gyare-gyare da asusunku, hanyar samun wannan shine canza sunan mai amfani.
Lokacin da aka canza sunan, asusun da ya gabata ya daina wanzuwa, kuma mai amfani na iya shiga nan da nan tare da wannan kalmar sirri a ƙarƙashin sabon sunan. Ana iya canza sa hannu a shafukan tattaunawa da hannu idan ana so.
Duba Archive1 da Archive2 don cikakkun bayanai kan buƙatun da aka yi kafin jami'ai masu kula su sami damar aiwatar da wannan aikin.
Duba kuma
- Kulle account
- Manual:Renameuser
- Taimako:Sake sunan mai amfani Koyarwa ta Special:RenameUser tool
- Taimako:Unified login