Jump to content

Shafukan Wikipedia Masu Buƙatar Hoto 2022

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Wikipedia Pages Wanting Photos 2022 and the translation is 88% complete.
Outdated translations are marked like this.

Wikipedia Pages Wanting Photos 2022

Home Participating Communities Organizing Team Participate Results Resources FAQ & Campaign Rules

Wikipedia Pages Wanting Photos (WPWP) wato Shafukan Wikipedia Masu-buƙatar Hoto gasa ce ta duk shekara inda yan'Wikipedia daga kowane harsuna da al'ummu ke sanya hotuna a muƘalolin Wikipedia marasa hoto. Wannan dan a karfafa amfani da hotunan da ake samarwa ta shirye-shiryen gasannin ɗaukan hoto daban-daban da akeyi, photowalks wanda Wikimedia community ke shiryawa, a shafukan muƙalolin Wikipedia. Hotona sunfi jan hankalin mai karatu akan ace rubutu ne zalla, suna taimakawa wajen fayyacewa, da siffantar da bayanan da ke a muƙalar har ta zamo bayyananniya damin fahimtar masu karatu. Dubban hotuna anbayar dasu da sanya su a Wikipedia Commons, ta hanyar shirye-shiryen wayar da kai daban-daban kamar photowalks, da gasussukan da suka hada da gasannin daukar hoto na kasa-da-kasa kamar su Wiki Loves Monuments, Wiki Loves Africa, Wiki Loves Earth, Wiki Loves Folklore, da sauran su. Har yanzu kadan ne daga hotunan akayi amfani dasu a mukalolin Wikipedia. A ya u, Wikimedia Commons na dauke da miliyoyin hotuna amma kadan ne daga cikinsu suke a mukalolin shafukan Wikipedia. Wannan gibi ne mai yawa sosai wannan gasar keson kullewa.

Yadda zaku shiga gasar

Kafin shiga gasar, yana da muhimmanci ku karanta duk dokokin gasar da kuma ka'idoji. Rashin yin hakan zai iya sawa a cire ku a gasar.

  1. Ku duba idan kun cancanta ku shiga gasar. Any gyara ga ka'idojin cancanta na shekarar 2022; saboda haka duk masu shiga gasa ana bukatar ya zama sun kirkiri account kimanin shekara daya da ya wuce kafin gasar.
  2. Ku samo mukala wadda ke bukatar hoto. Akwai hanyoyi da dama na yin hakan.

Ga wasu daga cikin su.

  1. Nemo hoton da ya dace a Commons. Binciko hoton ta yin amfani da laƙabinsa ko category. Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya yin haka. Duba wannan yadda zaku yi. Anan ma akwai wasu ƙarin bayani. Ku sani cewa amfanin hoto shine ƙara fahimtar da masu karatu akan abinda muƙala ke magana akai, ta yin amfani da nuna mutane, abubuwa, ayyuka da wasu ababe da aka bayyana a muƙalar. Kuma dacewar muƙalar ta zama a fayyace. Hotunan su kasance masu muhimmanci da dacewa a abinda maƙalar ke magana akai, bawai kawai dan ayi kwalliya ba.
  2. A shafin article din, nemi wani yanki inda hoton ya dace kuma zai taimakawa mai karatu fahimtar batun. Latsa Edit ka saka hoton, sannan ku haɗa da takaitaccen bayani wanda yake bayanin abin da hoton yake nunawa a cikin labarin. Yi amfani da mafi kyawun hotuna masu samuwa. Hotuna marasa inganci - duhu ko dishi-dishi; nuna batun ma karami ne, ɓoyayye ne a cikin ɓoye, ko shubuha; da sauransu - kada a yi amfani da su sai dai in ya zama dole. Yi tunani a hankali game da waɗanne hotuna ne suka fi kwatanta batun. Kuma DOLE bayar da taƙaitaccen gyara ga duk gyararrakinku, "Preview" kuma ku yi kowane canje-canje da suka dace. Haɗa hashtag $wpwp a cikin taƙaitaccen taƙaitaccen bayanin duk abubuwan da aka inganta tare da hotuna. Sannan danna "Buga canje-canje". Da fatan za a duba: Jagora kan yadda za a yi amfani da Hashtags na Kamfen ɗin WPWP
  3. Ku kula sosai akan syntax na sanya hoto! Idan zaku sanya hotunan ne a infoboxes na muƙaloli, Shi sunan kawai na hoton — ne, bawai sanya wani [[File:Obamas at church on Inauguration Day 2013.jpg|thumb|The Obamas worship at [[African Methodist Episcopal Church]] in Washington, D.C., January 2013]] ko The Obamas at church on Inauguration Day 2013.jpg.

Syntax na files tare da gajeren bayani

A boy playing with a butterfly
Yaro yana wasa da Malam-bude-mana littafi.

Misali (Shike bada hoto a hannun dama):
[[File:Cute boy face with butterfly.jpg|thumb|alt=A boy playing with a butterfly|<translate>A boy playing with a butterfly</translate>]]

  • File:Cute boy face with butterfly.jpg Sunan hoton dole ya zama daidai (harda manyan wasali, ƙaidojin rubutu da tazara) kuma dole ya kasance yana da extension .jpg, .png ko da wasunsu. (Image: da File: suna aiki ɗaya.) Idan Wikipedia da Wikimedia Commons duka suna da hoto mai suna iri ɗaya, to na Wikipedia shine zai hau kan muƙalar.
  • thumb ana bukatar shi yanwancin lokuta
  • alt=A boy playing with a butterfly Alt text ana sanya shine ga waɗanda basa iya ganin hoton; ba kamar gajeren bayann hoto ba, shi yana bayani ne game da surar hoton . Dole ya dace da sharuddan accessibility kuma yayi nuni da shahararrun bukukuwa, mutane da sauran abubuwa.
  • A boy playing with a butterfly shine gajeren bayanin hoto kuma shi ke zuwa karshe. Yana kara bada haske ne akan abunda hoton ke magana akai.

Duba en:WP:Extended image syntax dan ƙarin bayanin abubuwa. Idan hoton bai bayyana ba bayan ka duba sunan, zai iya zama saboda an hana amfani da shi.

Ka'idojin gasa


Dole a sa hotunan a tsakanin 1 ga Yuli zuwa 31 ga Augustan shekarar 2022.

Ba kayyade ko hoto nawa mai shiga gasa zai iya sanya ba. Amma akwai rabe-raben kyaututtukan da za'a bada. Ana jan hankalinku kada kusa hotuna a cikin mukala inda bai dace ba. Ku sanya shi a article da baabu hoto kuma ya dace a sanya shi.

Dole ya zama hoton an samar da shine a kan lasisi na kowa zai iya amfani da shi ko kuma na al'umma.

An kayyade shiga gasar ga wanda suka kasance suna da account da yayi kimanin shekara guda. Domin samun damar shiga gasar, mai shiga dole ya zama yayi rajistar account dinsa (wannan zai iya kasance a kowane manhaja na Wikimedia) a ranar ko kuma kafin 1 ga Yuli na shekarar 2021.


Ba a da bukatar hotuna marasa inganci ko kuma marasa kyawu

  1. Gajeren bayanin hoton da kuma cikakken bayani su kasance a bayyane kuma suyi daidai da bukatar mukalar
  2. Dole kowane hoto ya zama yana da gajeren bayanin gyara wanda zai yi bayanin hoton ko na minene.
  3. Hotunan a sanya su inda ya dace a cikin mukalar.
  4. Kada ku dora hoto a Wikipedia dake yaren da baku ji sosai. Za'a iya cire wanda suka dora hotuna marasa caption ko kuma wanda basu da alaka da mukalar ita kanta.

Wanda ya shiga gasa dole yasa hashtag #WPWP a gajeren bayanin gyara ga duk articles din daya sama hoto, misali "Kyautata mukala da hoto" #WPWP. Kada ku sanya hashtag (#WPWP) a cikin mukalar. Ku duba Guide on how to use WPWP Campaign Hashtags

Jadawalin Gasa

  1. Ranar fara gasa: 1 ga July, 2022
  2. Ranar karshen gasa: 31 ga Augusta, 2022
  3. Fadin Sakamako: 27 ga Oktoba, 2022

Rabe-raben kyaututtuka na duniya

  • Kyaututtuka ga mutum ukku da suka fi kowa dora hotuna a Wikipedia
  1. Kyautar na daya - Kambin kyauta da kuma WPWP Souvenirs tare da Satifiket
  2. Kyautar na biyu - Kambin kyauta da kuma WPWP Souvenirs tare da Satifiket
  3. Kyautar na ukku - Kambin kyauta da kuma WPWP Souvenirs tare da Satifiket
  • Kyautar sabon user wanda yafi kowa dora audio a Wikipedia
  1. Kambin kyauta da kuma WPWP Souvenirs tare da Satifiket
  • Kyautar sabon user wanda yafi kowa dora video a Wikipedia
  1. Kambin kyauta da kuma WPWP Souvenirs tare da Satifiket
  • Kyautar sabon user wanda yafi kowa dora hotuna a Wikipedia
  1. Kambin kyauta da kuma WPWP Souvenirs tare da Satifiket

Wiki Loves Africa prize categories

  • 1st prize - US $80 gift card
  • 2nd prize - US $50 gift card
  • 3rd prize - US $30 gift card

PLEASE PUT #WPWP #WLA in your edit summary!

NOTE: THE PRIZES WILL BE AWARDED AS SCHOLARSHIP TOWARDS ANY UPCOMING ONLINE/OFFLINE WIKIMEDIA CONFERENCE

Visit Wiki Loves Africa 2022/WPWP to learn more.