Zaɓukan Gidauniyar Wikimedia/2022/FAQ
An tanada wannan shafin ne dan bayar da amsoshi ga tambayoyin da mutane suka fi yi game da Zaɓukan Kwamitin Amintattu. Sashunan da suke ƙasa suna ɗauke ne da tambayoyin gama gari akan Kwamitin Amintattu da zaɓukan Kwamitin Amintattu.
Idan kuna da tambaya da ba'a amsa ta a wannan shafin ba, ku taimaka ku aje tambayar a shafin tattaunawa. Tawagar masu gudanarwa da taimako a zaɓen mashawarta suna dubawa akai akai-akai shafin tattaunawar. Ku yi hakuri ku sani cewa wasu tambayoyi za'a aika sune zuwa ga Elections Committee dan bada amsar su. Masu gudanarwa zasu yi ƙoƙarin su wurin sadar da martani da aka samu.
Idan tambayar da wuri ake so ko kuma tana buƙatar a dakata ta, kuna iya tuntuɓar contact a facilitator directly.
Tambayoyin gama gari game da Mashawarta
Menene shi Kwamitin Amintattu?
Wikimedia Foundation Board of Trustees sune ke kula da ayyukan da Gidauniyar Wikimedia suke gudanarwa. Kwamitin Amintattu ya tattara ne da amintattun al'umma da na ƙungiyoyin da ake da alaƙa da su da kuma waɗanda aka zaɓa. Kowani amintacce zai yi aiki ne na tsawon shekaru uku. Al'umman Wikimedia zasu iya shiga cikin zaɓan amintattun al'umma.
Su wanene amintattu a Kwamitin?
Amintattun mutane daga ko'ina na duniya masu faɗaɗɗen ƙwarewa. Samu ƙarin bayani game da haka a who is currently on the Wikimedia Foundation Board of Trustees.
Amintattu nawa ne za'a zaɓa a wannan zaɓen?
Amintattu biyu za'a zaɓa a wannan zaɓen.
Menene matakin ƙwarewa da ake nema dan neman zama matsayin amintacce?
Babu wani ɓuƙatan da ake nema da ya wuce iya turanci. Kwamitin Amintattu na wallafa ƙwarewar da ake nema da ƙa'idar yin zaɓen ta kowace shekara. Waɗannan bawai matakai bane da zasu dakatar da wani sai dai dan sauƙaƙawa al'umma fahimtar menene amintacce yake buƙata dan aiwatar da aikin shi da kyau amatsayin mashawarci. Kwamitin ya yaɗa desired skills and experiences for the 2022 candidates da zasu kawo.
Tambayoyi game da zaɓen
Shin akwai matakan da ake buƙata dan yin zaɓen?
Ea, akwai. Kwamitin Zaɓe ne ke ƙayyade cancanta akan zaɓen. Tsarin da ake bi na waɗanda suka cancantan na nan a jere a Community Voting page.
Sau nawa zan iya kaɗan kuri'a?
A wannan dokar: Ma'aikaci ɗaya, kuri'a ɗaya. Domin cimma cancantan yin zaɓe, za'a irga jerin gudunmawar ka a dukkanin wikis, idan Wiki ɗin ka ne ko wani.
Idan kayi ƙoƙarin canza kuri'ar ka, zaka iya haka. Wannan zai iya sauya zuciyar ka ko idan kayi wani kuskure. Kawai ka sake yin zaɓen sai kuma zaɓen da kayi a baya zai goge.
Yaushe za'a ɗauki zaɓaɓɓun amintattun aiki?
Ana tsammanin ɗaukan su na ƙarshe aiki zai faru ne a watan Oktoba lokacin taron Kwamitin Amintattun.
Menene Kwamitin Zaɓuɓɓuka kuma me yasa suke tsaranta hanyar da ake kaɗan kuri'a a zaɓen?
Kwamitin Zaɓuɓɓuka sune ke kula da zaɓuɓɓukan al'umma na Kwamitin Amintattun Gidauniyar Wikimedia. Kwamitin zaɓuɓɓuka da waɗanda suka gabata su suna nan tun 2004. Kwamitin Zaɓuɓɓukan na ɗauke da ma'aikata masu sakai daga al'umma.
Wane irin hanyar yin zaɓe ne Kwamitin Zaɓe zai bi?
Kwamitin Zaɓuɓɓukan sun zaɓi amfani da tsarin kuri'a ɗaya wanda ake canjawa. Wannan tsarin na ba ƴantakara dama da su jera ƴantakara akan kawai ace sun zaɓi mutum ɗaya kacal. Gwada tsarin da wannan misalin mai daɗi da abinci maƙwalashen. Ta yaya zaka jera mafi sonka a abincin maƙwalashen nan? Wataƙila kamar haka:
- Cokulet
- cincin
- cake
Akan kawai ace ka zaɓi Cokulet shi kaɗai, zaka iya jera maƙwalashen ka bisa buƙatar da kake das shi. Idan wasu mutanen da yawa sun zaɓi wani maƙwalashen na daban, zaɓin ka ana iya tura shi zuwa wani maƙwalashen. Tare da tsarin zaɓe na mutum ɗaya, za'a duba sauran zaɓin da kake ɓukata koda ɗan takarar da kafi so ba'a zaɓe shi ba.
Ina son shugabanci! Ta yaya ne zan shiga cikin Zaɓuɓɓukan Kwamitin sosai?
Haka abu ne mai kyau! Yadda mambobin al'umma suka shiga ciki zaɓen sosai, hakane zaisa zaɓen yayi inganci sosai. Mambobin al'umma suna iya zama ƴan takara ko su shiga cikin Kwamitin Zaɓen. Idan ba haka kake so ba, wani babban hanya da zaka iya shiga cikin zaɓen shine ka zama Ma'aikacin sakai na zaɓen.
Ma'aikatan Sakai na Zaɓen suke kulle giɓi tsakanin Ƴan Kwamitin Zaɓe da tawagar dake aiwatarwa da taimakawa na zaɓuɓɓukan Kwamitin, da kuma dukkanin al'ummar. Suna baiwa mambobin al'umma damar kasancewa da shiga cikin zaɓuɓɓukan dan taimakawa wurin hidima ga tafiyar.