Jump to content

ZangonMatanWiki 2023

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page WikiWomenCamp 2023 and the translation is 98% complete.
Outdated translations are marked like this.

ZangonMatanWiki 2023 zai kawo mutane wadanda suke bayyana kan su a matsayin mata daga kasashe daban daban na kungiyar Wikimidiya, shugabanni daga wadannan al’ummomi kuma masu zurfin sani wanda kuma suka sa hannu sosai a batutuwan da suka shafi gendergap|bambancin jinsi. Jigon wannan shekara shine "Isa Wurare, Tashi Tsaye".

An kawo shawarar a wajen taron Wikimania-Stockholm a 2019. An tsara ainihin shawarar sannan an gabatar da girant a 2020. Ba’a samu gudanar da taron ba saboda annobar Covid. Wannan taro sake maimaita kuduri ne irin wancan tare da sabbin bita akan matsayin yanzu, matsaloli, da kuma bukatu.


Manufofin zangon

Mun kuduri samar da wadataccen sani da bayanai masu inganci, dabaru da kuma hadin gwiwa a tsakanin ma-halarta wajen bincike akan nan gaba. Mun mayar da hankali wajen kawo mata daga asali daban daban wajen halartar taron na kwana uku wanda suka kunshi muhimman bayanai, ganatarwa, bita da kuma tattunawa, masu mayar da hankali akan matsayi da kuma nan gaban mata a wannan kungiya tare da mayar da hankali na musamman ga cike gurbin jinsi. A yayin da gurbin jinsi ya zamanto daya daga cikin muhimman abubuwa da aka bayyana, wannan dandali zai taimakon wajen samar da matakai da suka dace da kuma taimako da ake bukata wajen fadada wannan yunƙuri.

Muna fatan samun wakilci mai yawa daga ko'ina cikin duniya, tare da abubuwan da za a raba da yawa. Kamar yadda jagorancin ya yi tasiri sosai ga mata 'yan Indiya Wikimedians bayan shirin "Wiki Women for Women Wellbeing" da shirin "Women Train the Trainer", muna so mu "'sauƙa haɗin kai da damar jagoranci don haɗin gwiwa tsakanin shugabannin motsi tare da irin wannan ko ƙarin shirye-shirye a duk faɗin duniya"". Ana sa ran wannan zai haifar da cibiyar sadarwa mai karfi na mata a duk faɗin duniya kuma zai taimaka wajen tsara ayyukan ko shirye-shirye masu tasiri, masu fa'ida da juna.

Daga sakamakon binciken da aka riga aka rufe, za mu iya ganin tsammanin al'ummomi a sarari kamar yadda akwai mafi yawan fifiko ga batutuwa kamar "'bambancin Jinsi a tsakanin editoci, jagoranci, da kuma bayanan yanar gizo"'. Tare da wannan sauran wuraren da aka fi so inda za’a dauk editoci (mata) kuma a riƙe su, "'aiki don yaki da cin zarafi da ƙirƙirar ƙungiyoyin tallafi masu inganci da amsawa. "'Za mu kuma ba da horo na Advance Wiki kamar, kimantawa na sakamakon shirin, nazarin bincike, kayan aiki, da dai sauransu"'.

Wannan binciken ya nuna batutuwan da mata Wikimedians ke fuskanta a duk faɗin duniya, yana buƙatar canji a cikin shirin aiki. Kididdigar binciken ta goyi bayan "'tsarin da tsara ayyukan nan gaba kamar yadda tsarin dabarun motsi na Wikimedia - 2030 . "'

Muna so mu "'halicci rukuni na mutane masu tunani iri ɗaya daga bangarori daban-daban da ƙwarewa, na mutane a cikin ƙungiyar Wikimedia da sauran ƙungiyoyi masu daidaitawa", waɗanda za su iya koyo daga juna kuma ba su iyakance taron zuwa tattaunawa kawai kan gogewa, nasarori da batutuwa ba, har ma da "'brainstorm don nan gaba ta hanyar mai da hankali kan yadda za mu iya fadada fa'ida ta hanyar tsara sabbin ayyuka da shirin aiki don rage gibin jinsi a cikin abun ciki da motsi. "'

Wurin

"'New Delhi, Indiya'

Muhimman kwanakin

  • Sakin fom ɗin bincike kafin taron - 07 Fabrairu 2023
  • Rufe fom ɗin bincike kafin taro - 28 Fabrairu 2023
  • Sakin Binciken Shigar da Al'umma 2 - 10 Maris 2023
  • Rufe Binciken Shigar da Al'umma 2 - 31 Maris 2023
  • Ranar fitar da fom ɗin tallafi - 13 Yuni 2023
  • Ranar rufe tallafi - 4 ga Yuli 2023
  • Kira ga kungiyoyi da zasu biya kudadensu don shiga taron - 27 Yuli 2023
  • Kira ga masu horarwa - 28 Yuli 2023 - Closed

Kafofin hulda ta yanar gizo

Bi mu a Facebook - WikiWomenCampi

Sanarwar Sirrin Bayanai : WWC 2023

A wajen Taron Matan Wiki na 2023, sirrikan ku da kuma tsaron bayanan ku na da matukar amfani a gare mu. Wannan Sanarwar Tsarin Tsaron Bayananku na nuna yadda muke tattara, amfani, da kuma kare bayanan ku na sirri kafin, a lokacin da kuma bayan taron.

Tattarawa da kuma Amfani da Bayanan ku na Sirri

  1. Bayanan Rijista: Idan kuka yi rijistan taron, zamu dauka bayanan ku na sirri kamar suna, adireshin imel, kungiya, da kuma kasa. Wannan bayanan na da muhimmanci a wajen sha’anin rijista da kuma don ciyar da ku da sabbin bayanai da bayanan da suka shafi taron.
  2. Halartar Taron: Za mu iya tattara bayanai game da zaman da kuka halarta yayin taron. Wannan bayanin yana taimaka mana mu fahimci abubuwan da masu halarta suka fi so da kuma inganta abubuwan da za su faru a nan gaba.
  3. Sadarwa: Muna iya tuntubar ku don jin albarkacin bakin ku, bincike, ko kuma muhimman sabbin bayanai da suka shafi taron ko kuma tarukan Wikimidiya da zasu faru nan gaba. Kuna iya zabar fita daga karbar sakonni a kowanne lokacin

Tsaron Bayanai da Ajiye su

  1. "'Na sirri:"' Mun aiwatar da matakan da suka dace na zahiri, fasaha, da na ƙungiya don kare bayanan sirri daga samun dama, asarar, ko canji ba tare da izini ba. Muna iyakance damar samun bayanan sirri ga ma'aikatan da aka ba da izini waɗanda ke buƙatar shi don dalilan da aka ambata a sama.
  2. "'Rarraba Bayanai:"' Ba mu siyarwa, kasuwanci, ko bayyana bayananku na sirri ga wasu mutane sai dai idan doka ta buƙaci ko kuma tare da yardarku. Koyaya, zamu iya raba bayanan da aka tara da kuma ba a bayyana su ba don dalilai na kididdiga.
  3. "'Ajiye Bayanai:"' Muna riƙe bayanan sirri muddin ya cancanta don cika dalilan da aka tattara shi ko kuma kamar yadda ake buƙata ta dokoki da ka'idoji masu amfani.

Hakkin ku

  1. "'Dama da Gyara:"' Kuna da 'yancin samun damar isa ko kuma gyara duk wani bayanin sirri da muke da shi game da ku. Idan kuna buƙatar taimako don yin haka, don Allah tuntuɓar mu ta amfani da cikakkun bayanai da aka bayar a ƙasa.
  2. "'Goge Bayani:"' Kuna iya neman share bayanan sirri. Koyaya, don Allah a lura cewa wasu wajibai ko kuma abubuwan da suka dace na iya hana sharewa nan take.
  3. "'Janye amincewa:"' Za ku iya janye yardar ku don amfani da bayanan ku a kowane lokaci. Wannan janyewa ba zai shafi halattaccen aiki bisa ga yardar ba kafin janyewa.

Bayanan Tuntuɓa

Idan kuna da wasu tambayoyi, damuwa, ko buƙatu da suka shafi bayanan sirri ko wannan Sanarwar ta Tsaron Bayanai, don Allah ku tuntuɓe mu ta hanyar imel a admin@wikiwomencamp.org

Sabbin Bayanai akan Sanarwar Tsaron Bayanai

Ana iya sabunta wannan Sanarwa akan Tsarin Bayanai daga lokaci zuwa lokaci don nuna duk wani canji a cikin ayyukanmu ko bukatun doka. Za a buga fasalin da aka sake sabuntawa a shafinmu kuma za a sanar da ku duk wani gagarumin canji kai tsaye.

Ta hanyar shiga cikin sansanin mata na Wiki, kun yarda da sharuddan wannan Sanarwa akan Tsaron Bayanan ku

Muna godiya ga amincewar ku kuma muna tabbatar muku cewa za mu kula da bayanan ku da kulawa da mutunta sirrikan ku.

An sabunta shi na ƙarshe: 30th Satumba 2023

Duba kuma